Rundunar Yan Sandan Nigeria Ta Ce Jarrabawar Daukar Sabbin Yan Sanda Cike Ta Ke Da Kura-Kurai.

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Najeriya – ƙarƙashin jagorancin Babban Sifeton ‘yan sandan ƙasar Kayode Egbetokun – ta ce za ta sake nazarin sunayen mutanen da suka yi nasarar jarrabawar shiga aikin ‘yan sandan ƙasar, wadda hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta ƙasar ta shirya.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce jarrabawar ɗaukar sabbin ‘yan sandan cike take ta kura-kurai.

A lokacin da aka saki sunayen ranar 4 ga watan Yuni, shugaban hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta ƙasar, Solomon Arase ya ce an bi ƙa’ida wajen tantance mutanen da aka fitar da sunayen nasu.

To sai dai Olumuyiwa Adejobi ya ce da yawa daga cikin sunayen da hukumar ta fiar ba su ma cike takardun neman aikin ba.

Mai magana da yawun rundunar ya ce bayan nazari mai zurfi, kan sunayen da hukumar kula da aikin ɗan sanda ta ƙasarta fitar a shafinta, rundunar ta gano kura-kurai masu yawa kamar haka:.

i) Mafi yawan sunayen ba su ma taɓa cike takardar neman aikin ɗan sanda ba, sannan ba su shiga kowane irin aiki na matakan ɗaukar aikin ba.

ii) Haka kuma wasu sunayen sun ƙunshi jerin mutanen da suka kasa samun nasara a jarrabawar kwamfuta ko suka yi rashin nasara a atisayen motsa jiki.

iii) Akwai kuma waɗanda aka cire kan matsalar lafiya da suke da ita, amma sai aka ga sunayensu cikin jerin sunayen da aka fitar.

vi) Babban abin tayar da hankalin kuma shi ne yadda aka yi zargin amfani da kuɗi ko cin hanci wajen fitar da sunayen, lamarin da ya sa sunayen waɗanda ba su cancanta ba suke fito a jerin.

Kan haka ne Adejobi ya ce babban sifeton ‘yan sandan ƙasar ya rubuta wa shugaban hukumar wasiƙar ƙin amincewa da sunayen, tare da aniyar sake nazarinsu.

Kwanaki shida bayan fitar da sunayen ne, shugaban ƙasar Bola tinubu ya sauke Arase daga muƙamin nasa, tare da maye gurbinsa da Hashimu Argungu, tsohon mataimakin babban sifeton ‘yan sandan ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *