Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya shawarci masu shirya zanga-zanga da su sake tunani gabanin fara zanga-zangar.
A yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja babban birin ƙasar a yau Juma’a, Egbetokun ya ce rahotannin sirri sun tabbatar musu sojojin hayar ƙasashen ƙetare na shirin shiga zanga-zangar.
Sai dai shugaban ‘yan sandan bai yi wani ƙarin bayani kan zargin shigowar sojojin hayar ƙasashen ketare ba cikin zanga-zangar.
“Muna bibiyar yadda lamura ke faruwa kan zanga-zangar da take mana barazana, yayin da wasu ƙungiyoyi ke neman a yi zanga-zangar tashin hankali irin ta Kenya, wasu kuma na kira a kwantar da hankali a yi ta cikin nutsuwa ba tashin hankali.
“Wasu na kiran a yi zanga-zangar nutsuwa amma da kausasan kalamai, wani abu da yake sa mu nazari kan gaskiyar lmarinsu. Muna da tarihin zanga-zangar da aka yi ta rikici a Najeriya. A ganina ya kamata mu kalli wasu zanga-zangar da ake yi a wasu ƙasashen da suka zama masu haɗari.
“Muna kira ga ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su janye daga wannan zanga-zanga, saboda illar da ke cikinta da ta fito ƙarara da kuma rashin sani ga matasan da suke kira a yi tashin hankali,” in ji Egbetokun.
Wasu matasa ne ke shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar daga 1 gawatan Agusta zuwa 15, saboda tsadar rayuwa.