Rundunar Yan Sandan Nigeria Za Ta Kare Ma Su Shirin Yin Zanga-Zanga Idan Ta Lumana Ce.

Spread the love

Babban sufeton ‘yansadan Najeriya ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar zanga-zangar da wasu ‘yan ƙasar ke shiryawa a wata mai zuwa, yana mai cewa “za mu kare masu zanga-zanga matuƙar dai ta lumana ce”.

Sai dai da yake magana bayan ganawa da manyan jami’an rundunar na faɗin Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi kira ga matasa da haƙura da zanga-zangar “saboda gwamnati na bakin ƙoƙarinta”.

“Idan zanga-zangar ta lumana ce za ku ganmu muna kare masu zanga-zangar. Ba mu adawa da zanga-zangar lumana, za mu taimaka wa masu zanga-zangar lumana saboda ‘yancinsu ne” in ji shi lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

“Amma kuma akwai alhaki a kanmu na kare rayuka da dukiyoyi. Ba za mu zauna muna kallon ‘yandaba suna ƙona gine-gine da sunan zanga-zanga ba, ba za mu yarda da wannan ba.”

Ya ƙara da cewa sun samu bayanan yadda wasu ke kiran matasa su kwaikwayi irin zanga-zangar da mutanen Kenya suka yi “kwabo da kwabo” a Najeriya.

“Ina amfani da wannan damar na yi kira ga matasan Najeriya, don Allah ku yi watsi da kiran duk wanda ke neman ku fito ku tayar da hankali. Tuni Najeriya ta ɗanɗana matsalolin mummunar zanga-zanga.”

Matasa na cigaba da tattaunawa game da zanga-zangar da masu shirya ta suka ce za a yi daga ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, musamman a shafukan sada zumunta.

Shi ma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar “su dakata tukunna har sai sun ji irin martanin zai mayar game da koke-kokensu”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *