Rundunar yan sandan Nijeriya ta cafke wanda ya kashe Nabeeha,

Spread the love

Yan sandan Najeriya sun tabbatar da kama wanda ya sace Nabeeha Al-Kadriyah da wasu mutane da ake zargi da hannu cikin satar mutane.

Kakakin ‘yan sandan Nijeriya ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Cikin sanarwar ya ce a wani samame da suka akai wani otel a yankin Tafa, a ranar 20 ga watan Janairu, sun cafke wani da ake kira Bello Mohammed, dan shekara 28, mutumin jahar Zamfara.

Duk Da Hada Layin Waya Da NIN Garkuwa Da Mutane Na Ci Gaba

“An kama shi da kuɗi da suka kai naira miliyan 2 da dubu dari biyu da hamsin, wanda muke zargin kuɗin fansa ne da wani wanda aka kama ɗan uwansa ya biya a yankin.

“Yayin gudanar da tambayoyi, mun gano cewa yana cikin gungun mutane da suka kama iyalan wani lauya da ake kira Ariyo a yankin Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairu, sannan suka kashe wata matashiya da ake kira Nabeeha,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kano: Hukumar KAROTA ta musanta wani rubutu da ta gani yana yawo da sunan ta

Wanda ake zargin in ji sanarwar ya yi tayin miliyan guda ga baturen ‘yan sandan yankin Tafa, sai dai DPO bai karbi kuɗin ba, ya yi aikinsa yadda ya kamata.

Babban sufeton yan sandan Nijeriya, ya ya bawa baturen yan sandan Tafa SP Idris Ibrahim, bisa halin kirki da ya nuna kan kin karbar na Goro, ya yi aikinsa bisa doka da oda.

Ba wannan ne karon farko ba, da ake yin kokarin bai wa jami’an yan sanda cin hanci amma suke kin karba, wanda hakan yake kara mu su kima da martaba a idon duniya.

Ko a shekarar 2023, sai da wani jami’an dan sanda a jahar , an yi masa tayin miliyoyin kudi , bayan kama wasu da ake zargi da aikata laifi, amma yaki karba.

Festulation Foundation ta koyar da mata 50 sana’o’in dogaro da kai bayan sun warke daga larular yoyon fitsari a Kano

Hakan ya sanya har tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karrama shi da nambar yabo, sannan hukumar daukar ma’aitan yan sanda ta Kasa ta kara masa matsayi zuwa mataimakin kwamishinan yan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *