Rundunar ƴansandan Najeriya ta gurfanar da ƴan ƙasashen waje masu aikata laifi ta intanet

Spread the love

Jami’an rundunar ƴansandan Najeriya da ke sashen kula da laifukan intanet, sun bankaɗo wani giungun ƴan ƙasashen waje da ke da hannu wajen aikata laifukan da ke da alaƙa da zamba ta intanet.

An dai kama waɗanda ake zargin ne a yankin Jahi da ke babban birnin Najeriya, Abuja.

A yayin gudanar da bincike, jami’an ƴan sandan sun kwato kayayyaki da dama daga hannun waɗanda ake zargin da suka haɗa da wayoyin hannu da kuma kwanfutoci iri daban-daban.

Rundunar ta gurfanar da ƴan kasashen wajen guda 113 da ake tuhumarsu da manyan laifuka da suka haɗa da zamba ta intanet da samun bayanan sirri ba bisa ƙa’ida ba da damfara ta hanyar tallace-tallace da halasta kuɗaɗen haram, da kuma shige da fice ba bisa ka’ida ba, a gaban babban kotun tarayya, da ke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *