Akalla dalibai dake karatun fannoni daban daban a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ‘Yan Asalin kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure 80 ne suka karbi tallafin karatu( Scholarship) na naira dubu hamsin hamsin daga wakilin kananan hukumomin a majalisar Wakilan tarayyar Najeriya *Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum*.
Da yake jawabi ga daliban yayin Mika musu wannan tallafi, Rurum Wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin bada tallafin karatu na Ofishin sa Kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bunkure Hon Rabi’u Bala yace an baiwa daliban tallafin ne da nufin rage musu kudin makaranta da Kuma tallafawa harkar karatunsu.
Rabi’u Bala ya Kuma ja hankalin daliban dasu maida hankali a karatun da suke tare da tunasar dasu cewar nan gaba zasuci moriyar sa.
Anasa Jawabin, Sakataren Kwamitin Alh Dauda Bala Me Nama Rano yace *Babban kudurin da Turakin na Rano yasa a gaba a Zangon nan nasa na biyu shine Bunkasa harkar Ilmi a kananan hukumomin guda uku.*
Ya Kuma shaida cewar hakan ce ta sanya tun zaman sa wakilin Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar Kasa Karo na biyu cikin watan Yunin Shekarar 2023n data gaba, ya himmatu wajen tallafawa daliban dake karatu a Jami’oi da kwalejoji dake fadin kasarnan, bayaga ginawa da samarda kayan koyo da koyarwa a makarantun firamare da sakandire dake kananan hukumomin..
Alh Dauda Me Nama ya bayyana cewar *dalibai kimanin 80 kwamitin bada tallafin ya tantance masu karatu a Jami’ar ta Ahmadu Bello Kuma kowannensu zai karbi tallafin naira dubu hamsin, inda jimillar kudin ya kai naira miliyan 4.*
Ko a kwanakin baya dai Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum ya bada makamancin wannan tallafi ga fiye da dalibai 100 ‘Yan Asalin Rano, Kibiya da Bunkure dake karatu a Jami’ar Bayero ta Kano da Kuma wasu cikin daliban dake karatu a kwalejojin da ake dasu a Jihar.
Cikin Farin ciki, wasu cikin daliban da suka Amfana da tallafin *Shamsu Saidu Barkum da Rabi’u Ibrahim Kibiya da Abdulhadi Ali Rano da kuma Firdausi Shehu Barde Bunkure* Sun bayyana matukar godiya da jin dadinsu da Tallafin karatun da Dan majalisar ya basu tare da cewar zasu cigaba da yi masa Addu’ar Allah ya kara daga matsayinsa ya Kuma jibanci lamarinsa kamar yadda ya himmatu wajen sauke nauyin al’umma da yake wakilta..
A cewarsu wannan ne Karo na farko da wani zababbe a yankin ya Kai musu irin wannan dauki duk kuwa da irin matsi da wahalar karatu da suke fuskanta..
*Fatihu Yusuf Bichi*
*Media Aide to the Member Representing Rano, Kibiya & Bunkure Federal Constituency, Abuja.*
*17/1/2024*