Rurum Ya Tallafawa Al’ummar Mazabar Sa Da Naira Miliyan 280.

Spread the love

Mutanen kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure sun bayyana farin ciki da Jin dadin tallafin kudi Naira Miliyan dari 280 da wakilin su na majalisar tarayya , RT Hon Kabiru Alhassan Rurum,ya Amince za’a fara tura mu su ta asusun bankuna.

RT Hon Kabiru Alhassan Rurum ya ce ya bullo da wannan tsari ne domin tallafawa Al’umma samun sauki halin wahalar rayuwa da ake ciki a wannan lokaci..

Wannan shine karo na biyu da , Rurum , din yake irin wannan tallafi da aka sawa suna Alert Empowerment domin ko a farkon wannan shekara ta 2024 anyi makamancin wannan tallafi da aka rabar da naira Miliyan 45 aka turawa Jama’a a kananan hukumomin guda 3.

A wannan tallafi kusan mutane dubu 2,500 ne zasu sami kudade Kai tsaye ta asusun bankunan su, Kuma mafi karancin kudin da za’a tura shine naira dubu 50, yayinda wasu zasu samu naira dubu 100 wasu 200 wasu 500 wasuma za’a Tura masu kudi naira Miliyan 1 wasu Miliyan 2 kamar yadda shugaban kwamitin rabon tallafin Kudin P .A Murtala Muhammad Sani, ya sanar yayin kaddamar da tallafin.

Fatihu Yusuf Bichi
Media Aide to Rurum

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *