Rundunar Yan Sandan Kano Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Nuna Kwarewa A Aiyukansu.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano ta bayyana cewa za ta ci gaba nuna Kwarewa da kuma bin Doka da oda, wajen gudanar da aiyukansu kamar yadda yake a dokokin kasa Nigeria.

Kakakin rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A wannan rana ce wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin fitar da Sarki Muhammadu Sanusi II daga fadar Kofar Kudu.

Kotun ta kuma umarci ‘yan sanda da su tabbatar da duk wani hakki da alfarma da ya kamata an baiwa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, a ci gaba da dambarwar masarautar Kano.

Sai dai kuma wata babbar kotun jihar Kano ta yi gargaɗi ga kwamishinan ‘yan sandan jihar da Sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya da darektan jam’ian tsaro na DSS da hafsan hafsoshin Najeriya da kuma sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da su guji cusgunawa Sarkin kano Muhammadu Sanusi II.

Takardar kotun mai ɗauke da sa-hannun rijistarar kotun, Umar Mustapha, ta yi ƙarin bayani kan abin da take nufi da cusgunawa da ta haɗa da ƙoƙarin fitar da Sarki Sanusi daga gidan Rumfa ko ƙwace tagwayen masu ko kuma duk wani abun da zai janyo wulaƙanci ga Sarkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *