Rushe Sarakuna: Radio Kano Ta Yi Mubayi’a Ga Matakin Majalisar Dokokin Jihar

Spread the love

Kano

Wasu daga cikin ma’aikatun gwamnatin jahar Kano, sun Fara cire hotunan Sarkin Kano na 15, daga ofisoshin su.

Gidan Radio Kano mallakar gwamnatin jahar , na daga cikin wadanda Suka Fara daukar wannan mataki na cire hotunan Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero.

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jahar Kano, akan gidajen Radio, Hon. Bashir Aminu Panshekara, ya tabbatar wa da jaridar idongari.ng, hakan a yau Alhamis.

Wannan na zuwa bayan da majalissar dokokin jahar Kano, ta amince da rushe duka masarautun jahar , bayan soke
sabuwar dokar da ta kirkiri sabbin masarautun a shekarar 2019.

Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Panshekara ya Kara da cewa Manajan Dirakta, na gidan radio Kano, Alhaji Abubakar Adamu Rano, ne ya bayar da umarnin cire hotunan , sakamakon majlissar dokokin jahar Kano, ta rushe masarautun jahar guda biyar da aka kirkira a shekarar 2019.

Idan har Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a kan sabuwar dokar hakan zai ba shi damar naɗa sabon sarki a masarautar Kano.

“Wannan doka ta bai wa gwamna iko, tun da an dawo da masarauta guda ɗaya, ya tuntuɓi masu zaɓen sarki su ba shi sunan wanda zai zama sarkin Kano,” kamar yadda Shugaban Masu Rinjaye na majalisar Kano Lawan Hussaini Dala ya yi bayani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *