Zababben dan majalisar dokokin Nijeriya dake wakiltar al’ummar kananan hukumomin, Rano Bunkure da Kibiya daga jihar Kano, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya tallafawa wasu yan jarida, don su gudanar da bukukuwan babbar Sallah cikin walwala da annushuwa kamar kowa.
Dan majalissar da yanzu haka yake kasar Saudiyya, don gudanar da aikin hajji bana na 2025, bai manta da yan jaridar ba, har ya bayar da sakon barka da Sallah aka kawo musu.
Yan jaridar sun nuna farin ciki da annushuwa tare da cewa wannan shi ne karon farko da wanni wakilin al’umma ya tallafa musu , kuma ba za su manta da alkairin da aka Yi musu ba.
A kalla mawallafa labarai a jaridu da masu Aiko da rahotanni kusan 20 ne suka amfana da tallafin Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum
Rurum, ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa Yan jaridar ta kowanne bangare, bisa gudunmawar da suke bayarwa Kai tsaye ga al’umma.
Ya kuma ce Yan Jarida mutane ne masu mutunci, a idon Duniya da Bai kamata ayi watsi dasu ba.
Rahotanni na cewa Dan majalissar shi kadai ne, cikin wakilan al’umma daga jihar Kano ya tallafawa yan jaridar.
Yan jaridar da suka samu tallafin Dan majalissar suna gudanar da aiyukan su ne jihar Kano, Inda suka gode masa tare da Yi masa fatan Alkairi da kuma yin hajji karbarbiya.