Ruwan Sama Ya Haddasa Barna A Ecuador

Spread the love

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa gagarumar ɓarna a ƙasar Ecuador, inda ya kashe aƙalla mutane shida.

Ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa sun lalata tituna da gadoji da gidaje a Quito babban birnin ƙasar da kuma larduna da dama.

Wakilin BBC ya ce zabtarewar ƙasa mafi muni ta faru ne a tsakiyar garin BanyoS Diyago Santa, inda ɗimbin ƴan kwana-kwana da masu aikin sakai ke neman waɗanda ake tunanin sun tsira.

An kwashe sama da mutane 200 daga wurin zuwa wasu matsugunai na wucin gadi da aka tanada.

Ana ƙara nuna damuwa game da zuwan wani sabon yanayi da tuni aka fara kira La Niña, da zai zo da ƙaruwar tsananin sanyi da ruwan sama mai ƙarfin gaske a ƙasashen yankunan Arewaci da kuma Kudancin Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *