Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba ya zayarci wasu unguwanni birnin Kano da ayyukan ‘yan daba ke ci wa tuwo a ƙwarya.
Kwamishinan ya ziyarci unguwannin da ke yankunan ƙananan hukumomin Gwale da Dala da kuma Kumbotso.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce kwamishinan ya gana da masu ruwa da tsaki a unguwannin tare da ziyartar ofisoshin ‘yansanda na unguwannin a ƙoƙarin kakkaɓe matsalar daba da ke addabar wasu unguwannin birnin.
Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ayyukan ‘yan daba ke ƙara mamaye wasu unguwannin birnin.
Sabon kwamishinan ya ce matsalar daba annoba ce da kowa ya kamata ya bayar da gundumowa wajen magance ta.
”Don haka muke kira ga kowa ya tallafa ta hanyar da yake ganin zai iya domin magance wannan matsala da ta addabi Kano”, in ji sanarwar.
Kwamishinan ya kuma tabbatar wa al’ummomin unguwannin Dala da Dorayi da Sharada-Ja’in cewa rundunar ‘yansandan za ta yi duk a in da ya dace don kare lafiyarsu daga hare-haren ‘yan dabar.
A baya-bayan nan dai matsalar ‘yan daba ta sake dawowa a birnin Kano, lamarin da ke ƙara jefa fargaba a zukatan mazauna wasu unguwannin birnin.
A makon da ya gabata ne dai gwamnan jihar nuna damuwarsa kan yadda ayyukan ‘yan daba ke neman dawowa a jihar.