Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda CP Ahmed Musa, da zai jagoranci rundunar.
Wannnan dai na zuwa bayan ritayra da CP Ali Hayatu Kaigama ya yi daga aikin yan sanda baki daya.
CP Ahmed Musa dan karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa ya zo Sakkwato domin aikin kare mutanen jiha da dukiyoyi da kasa baki daya.
Sabon kwamishinan yan sandan jahar ya fara aikin dan sanda a shekarar 1994 da mukamin ASP bayan kammala makarantar yan sanda ta garin Wudil Kano, kuuma ya fara aiki ne a jahar Kogi.