Sabon Rikicin Siyasa Ya Kunno Kai Tsakanin Gwamna Uba Sani Da Nasir El-Rufa’i.

Spread the love

Wani rikici irin na siyasa ya kunno kai a jihar Kaduna da ke tsakiyar Najeriya, bayan da Gwamnan Jihar Uba Sani ya ce gwamnatinsa ba za ta iya biyan ma’aikata albashi ba saboda gagarumin bashin da ya gada daga Malam Nasir El-Rufa’i

Yayin wani taro da ya gudana a ranar Asabar a Kaduna, Uba Sani ya ce ya gaji bashin dala miliyan 587 kwatankwacin naira biliyan 85 ga kuma kudin kamfanonin ‘yan kwangila 115.

Ya ce an cire biliyan bakwai cikin 10 na kason da gwamnatin tarayya ta bai wa Kaduna a watan Maris biliyan bakwai ta tafi a biyan bashi.

Inda ya ara da cewa abin da ya yi wa jihar saura shi ne biliyan uku, ita kuma jihar tana biyan albashin biliyan 5.2 ne duk wata.

Ya ce tashin canjin kudi ya sanya jihar na biyan ninki uku na bashin da aka ci a baya.

“Duk da bashin da mukatarar da ya yi mana kanta, amma gwamnatina ba ta aro ko kobo ba a cikin watanni 9 di muka kwashe muna shugabanci

Waɗannan kalamai dai sun janyo martani daga ‘yan siyasar ciki da wajen jihar, kuma cikin waɗanda suka yi martanin har da ɗan El-rufa’i Bashir.

Bashir El-Rufa’i ya rubuta a shafinsa na X cewa gwamna Uba Sani na neman fakewa da bashin ne ya rufe gazawa da kasawar gwamnatinsa.

Bashir ya yi ikirarin cewa gwamnan na neman sauka daga kai ayyukan da aka zaɓe shi a kai ya manta da aikin da ke gabansa,

“Wadannan sun tabbatar da cewa ba su cancanci wannan mulkin ba baki ɗaya kuma hanya guda da za su boye hakan shi ne dauke hankalin mutane. Daga gwamnan da ya tare a Abuja ko da yaushe ya ke barci zuwa muƙarrabansa da aka naɗa muƙamai saboda dalilan siyasa na shiririta,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

Wannan dambarwa ta sanya mutane tunanin ko an sa zare ne tsakanin gwamna mai ci da wanda ya gaba?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *