Sabon Shugaban EFCC Shiyar Kano, Ya Jinjina Wa Kwamishinan Yan Sandan Jahar CP M.U Gumel Na Wanzar Da Zaman Lafiya.

Spread the love

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya karbi bakoncin sabon shugaban hukumar yaki da hana cin hanci da rashawa ta kasa EFCC , shiyar jahar Kano, CE.Ibrahim Shazali , a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai.

A cewar Shazali , dole ne ya bayyana Farin cikin sa a madadin sauran ma’aikatan hukumar EFCC, kan yadda Kwamishinan Yan Sandan, yake taimaka mu su, musamman wajen kai sumamen Kama mutanen da ake zargi da yin chanjin kudaden ketare ba bisa ka’ida ba.

Sabon shugaban hukumar EFFC, CE. Ibrahim Shazali, ya bayyana cewa, ziyar ta kulla Zumunci ce, da kuma ya ba wa Kwamishinan sakamakon yadda ya ke gudanar da Aiyukan sa, bisa gaskiya da rikon amana Wanda al’umma suka shaida hakan.

Kakakin rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa, da ya aike da manema labarai a birnin Kano.

CE. Ibrahim Shazali, ya Kara da jinjina wa Kwamishinan Yan Sandan CP Muhammed Usaini Gumel, saboda yadda ya jajirce wajen tabbatar da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, duk da dambarwar da ta ke faruwa ta masarautun Kano.

 

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayyana Farin cikinsa da wannan ziyarar, tare da alkawarta cewa rundunar Yan Sandan da kuma hukumar EFCC tamkar Danjuma ne da Danjummai, wajen yin duk mai yiwuwa don tabbatar da an samu nasarar da ake da bukata.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *