Sabon shugaban Laberiya, Joseph Boakai ya gaza kai ƙarshen jawabin shan rantsuwarsa yayin da ya kusa shiɗewa, inda aka rirriƙe shi a lokacin bikin wanda ya gudana a Monrovia, babban binrin ƙasar.
Kafin nan ya kwashe kimanin minti 30 yana jawabi, inda daga baya magana ta fara yi masa wuya.
Daga nan ne masu tsaron shi suka tattarbe shi tare da mayar da shi gida daga babban zauren majalisar dokokin ƙasar, inda bikin ya gudana.
Daga nan ne aka kammala taron ba tare da an kai ƙarshe ba.
An rantsar da sabon shugaban ƙasar na Laberiya mai shekara 79 a duniya ne a matsayin shugaba mafi tsufa a ƙasar, inda ake da tantama kan ƙoshin lafiyarsa.