Sabuwar 2025: An Tsaurara Matakan Tsaro A Muhimman Wurare A Kano
Hukumomin tsaro a jahar Kano, sun Sanya shingayen bincike
don tabbatar da tsaro da ci gaba da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyin su, sakamakon murnar da jama’a ke yo cikin daren yau na shiga sabuwar shekarar 2025 t
Wakilin jaridar idpngari.ng, ya ga yadda jami’an Yan Sanda da civil defense harma jami’an bijilanti a wasu daga cikin sassan kwaryar birnin suka mamaye titina, don bayar da tsaro.
Sai dai wakilin Jaridar ya ce matasa na ta tururuwar fitowa daga Mabambantan unguwanni , Inda suka Yi cirko-cirko akan Tituna, musamman akan titin zuwa gidan Gwamnatin Kano da titin gidan Zoo da kuma wasu daidaikun Tituna.
Haka zalika an ga Tarin jami’an Yan Sanda akan Tituna da sauran muhimman wurare, don tabbatar da tsaro a fadin jahar.
Wasu daga cikin matasan na ta guje-guje da Ababen hawa , ya yinda wasu kuma ke kara ingiza su, Amma dai jami’an tsaron suka Yi.
Sannan wakilin jaridar ya ga motocin hukumar Hisbah ta jahar Kano, a cikin daren wadanda suka nufi wasu gurare, da Ake gudanar da bukukuwan musamman a karamar hukumar Nasarawa.