Shugabar kwamitin yiwa daurarru afuwa a jihar Kano dake arewacin Najeriya Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta shawarci al’umma da su dinga taimakawa daurarrun dake gidan gyaran halin jihar.
Hajiya Azumi ta bayyana hakan ne a yayin zantawar ta da manema labarai a Kano, albarkacin karatowar karshen shekarar 2024 da muke bankwana da ita.
Ta kuma kara da cewa gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf na sane da daurarrun, kasancewar akwai tanade-tanade da ya ke yi musu a kowanne yanayi da ake ciki.
- Da Me Shugaban Nijar Ya Dogara A Zargin Najeriya Da Faransa Da Yunƙurin Afka Wa Kasarsa?
- Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kitsa Fadan Daba Tsakanin Matasan Zango Da Kofar Mata.
Haka kuma ta yabawa gwamnan da mataimakin sa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a bisa yadda su ke gabatar da ayyukan alheri ga al’ummar jihar na birni da karkara.
A karshe ta yi fatan al’umma zasu dauki shawarar da ta basu, domin ya zama an dada sanya walwala a zukatan mazauna gidajen gyaran halin dake fadin jihar Kano.