Mataimakin sufeton yan sandan Nijeriya dake jagorantar shiya ta daya a jahar Kano, AIG Umar Sanda, ya yi kira ga jama’a su ci gaba da bayar da hadin kai ga jami’an yan sanda don dakile dukkan wata barazana da ta shafi harkar tsaro a Kano da Jigawa.
AIG Umar Sanda ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Radio Magazine Program Forum ,masu gabatar da shirin hatsin bara a gidajen radion jahar Kano .
AIG Sanda ya ce, a duk lokacin da al’umma suka ga wani da ba su amince da shi ba , su sanar wa da jami’an yan sandansu dan daukar matakin da ya dace.
Ya kara da cewa, idan al’umma basu sanar musu ba, ba za su iya sanin komai akai ba, kuma irin hakanne yake kawo rashin zaman lafiya a gari , sakamakon rashin daukar mataki tunda wuri.
Sai dai ya ce , aikin su ,shi ne kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu a koda yaushe, har ya jaddada muhimmancin zaman lafiya na wanzuwa ne ta hanyar bai wa yan sanda bayanan sirri da za su taimaka wajen dakile aiyukan batagari.
Kungiyar Radio Magazine Program Forum, ta kai ziyarar ce domin kulla alakar aiki da jami’an yan sanda, tare da lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen ci da tabbatar da tsaro ta hanyar ilimantar da al’umma, muhimmancin zaman lafiya da kaucewa daukar doka a hannu.
Kungiyar ta ce shirye ta ke ta yi aiki da rundunar yan sandan Nijeriya shiya ta daya Zone 1 , dan gannin an samu wanzuwar zaman lafiya mai dorewa.