Sai da muka rika sayar da kwandon tumatur 1,000 saboda rufe boda’

Spread the love

Tun bayan sanar da matakin janye takunkumin da ECOWAS ta sanya wa ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso al’umma ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu mabanbanta.

Mafi yawan wadanda BBC ta tattauna da su sun bayyana farin cikinsu da wannan mataki, suna cewa rayuwa ya kamata ta ci gaba kamar yadda take a baya.

Wani mutumi da ke zaune da iyalansa a kan iyakar Najeriya da Nijar, ya ce suna kai kayansu Kasuwar Magama da ke yankin jibiya amma sai da wajen ya zama tamkar kufai.

Gwamnan Oyo Ya Rufe Kamfanin Hakar Ma’adinan ’Yan China

Al’umomin Nijar Na Maraba Da Matakin ECOWAS Na Janye Wasu Takunkumai

“Kayan gwari muke kai wa, a baya sai da yakai duk kyau da girman tumatur kwandonsa baya wuce naira dubu ɗaya, kuma duk da haka babu mai saya.

“Tun daga nan manoma suka shiga mugun hali. shi yasa muka ji dadin wannan taki na janye wannan takunkumi don muna sa ran zai zama alkhairi,” in ji mutumin.

Cikin takunkuman da aka janye har da na buɗe iyakokin tuddai da na sama tsakanin kasashen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *