Sai yau Litinin muka karɓi umarnin kotu kan sauke Aminu Ado – Gwamnatin Kano

Spread the love

Yayin da ake cigaba da dambarwar saukewa da ɗora sabon sarki a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, gwamnatin jihar ta ce sai a ranar Litinin ta samu umarnin da ke hana ta rusa sababbin masarautu huɗu.

ranar Juma’a da dare ne Aminu Ado Bayero ya koma Kanon bayan balaguron da ya yi a kudancin Najeriya, inda ya tarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga gadon sarautar garin tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar.

Gwamnan ya ɗauki matakin ne jim kaɗan bayan Majalisar Dokokin Kano ta rushe dokar masarautu da aka ƙirƙira a 2019, wadda ta ƙirƙiro sababbin masarautu huɗu.

Wannan ta sa Aminu Babba, mai muƙamnin sarkin dawaki babba a masarautar, ya kai ƙara wata kotun tarayya wadda ta ba da umarnin a dakatar da sauke Aminu Ado, da naɗin Sanusi a matsayin sarki, sannan a bar abubuwa a yadda suke har sai ta kammala sauraron ƙarar.

Sai dai kuma, gwamnatin Kanon ta bakin Kwamashinanan Shari’a Haruna Isa Dederi, ta ce sai bayan sun aiwatar da duk abubuwan da kotun ta hana sannan suka ga umarnin nata.

“Wannan umarni da ake ta yamaɗiɗi a kai sai a yau [Litnin]…da misalin ƙarfe 10:00 na safe sannan ma’aikacin kotun tarayya a nan Kano ya kawo min shi,” in ji shi.

“Tun da yau ce ranar aiki kuma sai yanzu muka karɓa, to sai a saurari abin da kotun za ta ce idan muka tura namu takardun [martanin].”

Wakilin BBC a Kano ya yi yunƙurin jin dalilin da ya jawo jinkiirin isar umarnin kotun daga ɓangaren waɗanda suka shigar da ƙara amma bai yi nasara ba.

Yanzu haka dai Muhammadu Sanusi II na zaman fada a babban gidan sarki na cikin gari, yayin da shi kuma Aminu Ado Bayero ke nasa zaman a gidan sarki da ke unguwar Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *