Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Abdullahi Baffa Bichi ya nesanta kansa daga zargin da ake masa na jagorantar kungiyar Abba-Tsaya-da-kafarka.
Alhaji Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana haka ne Jim kadan bayan da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci sulhunta tsakanin sakataren gwamnati da Alhaji Hamza Maifata a gidan gwamnati.
” Ni Jarumi ne ba wanda nake tsoro dani na kafa kungiyar da zan fito na fadawa duniya, domin a duk duniya yanzu ba wanda nake tsoro”. Inji Baffa Bichi
Alhaji Abdullahi Baffa Bichi Wanda ya jaddada biyayyarsa ga gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce zai ci gaba da biyayya ga gwamnatin Kano da jamiyyar NNPP.
A nasa bangaren Dantakarar shugabancin karamar hukumar Bichi Alhaji Hamza Maifata Bichi ya ya bayyana gamsuwarsa da sulhun da aka yi tare da alwashin wani sabani ba zai Kara shiga tsakaninsu ba a nan gaba.
A nasa shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano. Alhaji Lawan Hussain Chediyar Yangurasa ya ce wasu makiya Jam’iyyar jihar Kano ne suke kokarin haddasa rikici a jihar Kano domin biyan bukatun Kashin kansu.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a Kwanakin nan ne dai wata kungiya ta bulla mai suna Abba tsaya da kafarka wadda aka zargi Sakataren gwamnatin da daukar nauyin kungiyar.