Ɗan majalisar dattawan Najeriya mai wakilitar Anambra da Kudu Ifeanyi Uba ya rasu.
Cikin wata sanarwar da mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon. Benjamin Kalu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ya kaɗu da mutuwar Sanatan.
Rahotonni sun ce marigayin ya fice daga Najeriya zuwa Birtaniya domin duba lafiyarsa, kwana biyu da suka gabata.
A shekarar da ta gabata ne Sanata Ifeanyi Ubah ya fice daga jam’iyyarsa ta YPP zuwa APC mai mulkin ƙasar.
Mutuwar ɗan majalisar na zuwa ne kwana biyu bayan rasuwar shugaban ƙungiyar kare muradun ‘yan ƙabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, Chief Emmanuel Iwuanyanwu.