Sanata Kawu Sumaila Ya Bayyana Cewa Duk Wata Yana Samun Naira Miliyan 21

Spread the love

Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila daga Kano ta Kudu, ya bayyana cewa yana samun fiye da Naira miliyan 21 a kowane wata a matsayin kuɗaɗen gudanar da harkokin ofishinsa.

A cikin wata hira da ya yi BBC Hausa, ya bayyana cewa albashin da Sanata ke karɓa bai kai Naira miliyan ɗaya, sakamakon cire-cire da ake yi wa albashin.

“Kuɗin da ake karɓa na albashi a wata bai kai naira miliyan ɗaya ba, idan an yi yanke-yanke yakan dawo kamar naira dubu ɗari shida da ɗan wani abu a matsayin albashi,” in ji shi.

Sai dai ya ce idan aka haɗe jimillar kuɗin da yake samu ya haura Naira miliyan 21.

“Saboda ƙari da aka samu, a majalisar dattawa ana ba wa kowane sanata naira miliyan ashirin da ɗaya a kowane wata a matsayin kuɗin gudanar da ofis ɗinsa.

“Ni dai ban san wani kuɗi da aka halarta ake ba ni a matsayin sanata ba,” a cewarsa.

Wannan bayanin na zuwa ne kwana guda bayan da Hukumar Kula da Albashi da Rarraba Kudi (RMAFC), ta ce kowane Sanata yana samun kimanin Naira miliyan 1.06 a kowane a matsayin albashi.

Shugaban RMAFC, Mohammed Shehu, ya yi wannan bayani a matsayin martani kan yadda ake biyan ’yan majalisar maƙudan kuɗaɗe.

Kawu ya bayyana cewa Naira miliyan 21 sun haɗa da kuɗin gudanar da ofis, kuɗin jaridu, tafiye-tafiyen cikin gida, da sauransu.

Ya nuna cewa a zahiri albashin ya kasa kai Naira miliyan ɗaya, amma idan aka yi cire-cire abin da yake ragewa bai wuce Naira 600,000 ba.

Idan ba a manta ba, tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ne, ya caccaki yawan kuɗaɗen da ’yan majalisa ke samu.

Sai dai, Sanata Kawu, ya caccaki Obasanjo, inda ya ce a zamanin mulkinsa ne aka fara ba ’yan majalisa kuɗaɗen da suke wuce hankalin mutane da nufin gyara ga kundin tsarin mulki domin sahalewa Obasanjo yin tazarce, zargin da a baya tsohon shugaban ƙasar ya musanta

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *