Sanatocin yankin Igbo sun nemi a sake duba ƙudurin harajin Najeriya

Spread the love

Sanatocin yankin kudu maso gabas sun shiga sahun waɗanda suke kira da a sake duba ƙudurorin haraji da shugaba Tinubu ya aika majalisa.

Jagoran gamayyar santocin yankin, Sanata Enyinnaya Abaribe (ɗan jam’iyyar APGA, mai wakiltar Abia ta kudu) ne bayyana hakan ga manema labarai bayan taron sanatocin daga jihohi biyar na yankin kudu maso gabas a ofishinsa.

Abaribe ya ce sanatocin yankin ba suna cewa a yi watsi da ƙudurorin ba ne, suna so a faɗaɗa tattaunawa, sannan a samu ƙarin lokaci domin su samu damar ganawa da waɗanda suke wakilta da sauran masu ruwa da tsaki kafin a ɗauki wani mataki a game da ƙudurorin.

Ya ƙara da cewa, “mun yi nazarin ƙudurorin sosai, sannan mun yanke shawarar cewa akwai buƙatar mu ƙara tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki daga yankin kudu maso gabas. Muna so yi hakan ne domin tabbatar da cewa ƙudurorin sun yi amfani ga ƴan Najeriya, musamman yankinmu,” in ji Abaribe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *