Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

Spread the love

 

Fitaccen lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Femi Falana SAN, ya ce ya la’akari da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a bayan nan, ya zama wajibi Sarki ɗaya tilo ne zai kasance a Jihar Kano.

Falana wanda ya faɗi hakan a cikin wani hoton bidiyo da ya karaɗe dandalan sada zumunta, ya kuma bayyana Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II a matsayin halastaccen sarki kuma zama daram duk da tababar da ake yi dangane da rikicin Masarautar Kano

Falana ya bayyana cewa “dole ne mu faɗa wa kanmu gaskiya a matsayinmu na lauyoyi. Saboda haka ina taya Mai Martaba murna dangane da nasarar da ya samu a Kotun Ɗaukaka Ƙara.

“Dole ne a fahimci tanadin da doka ta yi dangane da hurumin kowacce kotu dangane da mas’alar da ta shafi masarauta.

“Abu na biyu kuma shi ne Kotun Tarayya ba ta hurumi kan abin da ya shafi masarauta, saboda haka idan ma har akwai wasu lauyoyi da ke ganin Kotun Ƙoli na abin faɗa a wannan lamari to kuwa suna yaudarar waɗanda suke wakilta.

“Ire-iren waɗannan lauyoyi suna kawo matsala a ƙasar nan kuma nauyi ya rataya a wuyan Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta shiga ta yi ruwa da tsaki domin a yi wa tufkar hanci.

“Mai Martaba [Sarki Sanusi] ya sani cewa duk ma inda waɗannan lauyoyi za su je, kana nan zama daram a kujerar mulki kuma dole Sarki ɗaya tilo ne a Kano.

“Ba zai yiwu a ce akwai sarakuna biyu ba ne a Kano ko Shugaban Majalisar Dokoki biyu a Ribas. Dole ne a kawo ƙarshen wannan ruɗani.”

Ana iya tuna cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi soke masarautun Jihar Kano.

Kotun a hukuncinta na farko ta ce Babbar Kotun Kano ce kawai take da damar yanke hukunci kan duk wani ruɗani da ya shafi sarauta a jihar.

Sai dai an samu saɓani tsakanin alƙalai uku da suka yanke hukunci kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *