Sanya sojoji cikin rikicin masarautar Kano kuskure ne – Atiku

Spread the love
ATIKU

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce matakin gwamnatin tarayyar ya sabawa kundin tsarin mulki.

Ya ce matakin gwamnatin tarayya na tura jami’an tsaro Kano kan tirka tirkar da ake a game da batun nadin sarki abu ne da zai iya janyo matsala ga zaman lafiya a jihar, sannan kuma ya sabawa kundin tsarin mulki na 1999.

Atiku ya ce, a kokarin aiwatar da aikin da doka ta amince musu na samar da doka, majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar masarautar Kano ta 2024, daidai da sashe na hudu na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, yayin da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar.

Ya ce a don haka tura sojoji Kano a kan lamari irin wannan ya na rage wa sojoji kima.

Atiku Abubakar, ya ce ya kamata mu tunatar da Tinubu cewa Kano jiha ce da ta kwashe dubban shekaru tana cikin zaman lafiya kuma duk wani yunkuri na kawo fitina ba zai samu karbuwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *