Sanya Tuta A Gidan Sarki Na Nasarawa Yunkurin Neman Tsokane Ne: Gwamnatin Kano.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da tutar da aka sanya a gidan sarkin na Nasarawa, inda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune, a matsayin wani yunkuri na neman tsokana.

Tuta tana nuna karfin iko ne, sannan kuma tana nuna cewa sarki yana gida ko baya nan. Bisa al’ada ana tashin tutar da karfe 6 na safe kuma a sauke ta da karfe 6 na yamma, ana kuna sauke ta baki daya idan sarki ya yi tafiya.

A ranar Alhamis ne aka aka sanya tutar da karfe shida na safe a gidan sarkin Nassarawa.

Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II ko wanne a cikin su yana ikirarin cewa shi ne halastacce sarkin kano .

Gwamnatin jihar kano dai ta ce ta tsige Aminu Ado Bayero, sannan ta ce ta nada Sanusi II bayan rushe dokar da ta shafi masarautu wadda tsohon gwamnan kano Ganduje ya yi mata gyara a shekarar 2019.

Haka kuma ana tashin irin wannan tuta a fadar Gidan Rumfa, inda Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ke zaune.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi watsi da matakin a matsayin wani yunkuri ne kawai na jan hankalin jama’a.

“kawai kokari ne na tallata kai da kuma neman tsokana, amma babu wata tantama ko rudani Sarki Sanusi ne Sarkin Kano,” kamar yadda ya shaida wa Aminiya a jiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *