Majalisar sarakunan arewacin Najeriya ƙarƙashin mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar lll, ta nuna damuwarta kan halin da ake ciki a Kano kan rikicin sarauta.
Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin hadin kan sarakunan arewacin ƙasar, wanda kuma shi ne sarkin Gummi, Alhaji Lawal Hassan Gummi, ta ce rikicin ka iya shafar tsarin sarauta a yankin.
”Majalisarmu na kira ga duka ɓangarorin su dubi masalahar zaman lafiya da kwanciyar hankali, su kai zuciya nesa, kasancewar batun na gaban kotu, don haka a kwantar da hankali”, in ji sanarwar.
Haka kuma Majalisar ta yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, a jihar Kanon.
- Tinubu zai fara bikin cika shekara guda a mulki da buɗe ayyuka a Legas
- Tsohon Shugaban EFCC Ibrahim Lamorde Ya Rasu
A ranar Alhamis ne gwamnan jihar ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi ll kan karagar sarautar Kano bayan majalisar dokokin Kano ta yi wa dokar masarautun jihar kwaskwarima.
Sai kuma wata kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da dokar, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin sauraron shari’ar.
To amma ranar Juma’a sai gwamnan jihar ya miƙa wa Muhammadu Sanusi ll takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano.
Sai kuma kwatsam! A ranar Asabar aka wayi gari da wani turka-turka, bayan da Alhaji Aminu Ado Bayero wanda shi ne sarki kafin gyaran dokar, ya koma birnin tare da shiga gidan sarki da ke unguwar Nassarawa, bayan da Muhammadu Sanusi ll ya shiga fadar sarkin da ke Ƙofar Kudu.
Da safiyar Asabar ɗin ne dai gwamnan jihar ya umarci kwamishinan ‘yan sandan Kano ya kama Alhaji Aminu Ado bisa zargin yunƙurin tayar da tarzoma a jihar.
To sai dai kwamishinan ‘yan sandan ya ce rundunar ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro za su yi biyayya ga umarnin kotu.
- Tinubu zai fara bikin cika shekara guda a mulki da buɗe ayyuka a Legas
- Gidauniyar Tallafa Mata Ma Su Yoyon Fitsari ( Festula Foundation) Ta Koka Kan Rashin Yi Wa Mata Aiki Kyauta A Kano