Sarakunan Da Ke Danbarwar masarautar Kano Za Su San Matsayin su A Yau.

Spread the love

A Alhamis din nan sarakunan da ke shari’a kan Sarautar Kano za su san matsayinsu a gaban kotu.

Babbar Kotun Tarayya za ta yanke hukuncin ne kan dambarwar sabuwar dokar masarautun jihar, wadda ta tube Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da tawarorinsa na sabbin masarutu hudu da  tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Sabuwar dokar ta 2024 ta kuma dawo da tsohuwar Masarautar Kano tare da nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Bangaren Aminu Ado Bayero na rokon kotun ta soke sabuwar dokar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu, ta dawo da dokar Masarautun Ganduje wadda ta kirkiro Masarautun Bichi, Rano Karaye, Gaya, da kuma Kano.

Idan za a tuna, sabuwar dokar Abba da ta soke Masarautun Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudun ce ta ba da damar dawo da Sanusi II kan Sarautar Kano.

Hakan na zuwa ne shekara hudu bayan tube Sanusi II da Gwamnatin Ganduje ta yi, a lokacin yana Sarkin Kano na 14.

Daga cikin masu zaben sarki a Masarautar Kano, Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Danagundi, ne ya je kotu neman ta ayyana sabuwar dokar a matsayin haramtacciya kuma mara amfani, ta hannun lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN).

Bayan sauraron bukartar a ranar Juma’a, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya dage zaman zuwa Alhamis nan domin yanke hukunci.

A zaman na Alhami ne kuma alkalin zai yanke hukunci kan rokon dakatar da sauraron karar da wadanda ake kara suka shigar masa.

Daga cikin wadanda ake kara har da Gwamnatin Kano da Antoni-Janar kuma Kwamshinan Shari’an jihar, wadanda A.G. Wakil, ke karewa.

Sauran sun hada da majalisar dokokin jihar da shugabanta, wadanda Eyitayo Fatogun (SAN), ke wakilta.

A zaman ranar Juma’a majalisar da shugabanta sun sanar da kotun cewa sun shigar da bukatar daukaka kara, don haka akwai bukatar ta dakatar da nata shari’ar.

Amma alkalin ya bayyana cewa ba a kawo wa kotunsa wata hujja da ke nuna gaskiyar batun daukaka karar ba.

Bincikenmu ya nuna har zuwa ranar Laraba kotun daukaka kara ba da sa ranar sauraron karar da aka daukaka zuwa gabanta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *