Sarki Muhammadu Sanusi ll ya isa gidan gwamnatin Kano

Spread the love

Muhammadu Sanusi ll ya isa gidan gwamnatin Kano domin karɓar takardar kama aiki a hukumance a matsayin sabon sarkin masarautar Kano ɗaya tilo.

Rahotonni sun ce tun a cikin dare sabon sarkin ya isa Kano daga Legas inda ya zauna tun lokacin da aka tuɓe shi a shekarar 2020.

Za a gudanar da ƙwarya-ƙwaryan biki a lokacin miƙa masa takardar da za a yi a gidan gwamnatin jihar.

Ana sa ran sabon sarkin ne zai jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu.

Manyan hakiman Kano irin su Madakin Kano da Walin Kano da Sarkin Dawaki Mai Tuta da Sarkin Bai da Turaki duk sun hallara a ɗakin taron, domin shaida bikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *