Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulqadir Ya Kaiwa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, Ziyarar Barka Da Sallah a Dakin Taro Na Africa House Dake Gidan Gwamnatin Jihar ta Kano.
Dakta. Aliyu Ibrahim A Yayin Ziyarar tasa ya bayyanawa Gwamnan irin tsare-tsaren da Masarautar tayi acBangaren Tsaro, da Inganta Harkar Noma da Kiwo, da Ilimi, lafiya da kuma tsayawa kai da fata wajen yiwa Jiha da Kasa addu’ar Zaman Lafiya.
- Likitoci Sun Ciro Kifi Mai Rai Daga Cikin Wani
- Ta Sa Mata Guba A Ruwa Don Hana Ta Zuwa Hutun Haihuwa
Daga Nan, Mai Martaba Sarkin ya Kuma bukaci Gwamnan Jihar Kano daya Kawo Dauki Kan Matsalar Ruwan Sha da ta addabi Garin Gaya,da Kuma Samar da Makarantar Gaba Sakandire domin saukakawa matasan dake Karkashin Masarautar wajen yin karatun cikin sauki.
Da Yake Jawabi Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf,ya Godewa Mai Martaba Sarki bisa Wannan Ziyarar ta Karamci Daya kawo da alkawarin cika Koken al’ummar Mutanen Gaya da Mai Martaba Sarki ya isarwa Gwamnan.
Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya Kuma Baiyanawa Duniya irin alakar shi da Garin Na Gaya,inda yace Shima a Gaya aka Binne cibiyarsa.
Ya Kuma Riko Mai Martaba Sarki da aci gaba da Addu’ar Samun Dauwamanmen Zaman Lafiya Mai Dorewa a Jihar Kano
A Lokacin Ziyarar Mai Martaba Sarkin Ya Na tare da Daukacin Hakiman Masarautar ta Gaya Wadanda Suka Rufa masa baya Zuwa Fadar ta Gwamnatin Jihar Kano
Sa Hannun
Jami’in Yada Labarai Na
Masarautar Gaya
Auwalu Musa Yola
14/4/2024.