Mai Martaba Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim, ya kai ziyarar ta’aziyya ga wadanda gobarar masallaci ta shafa a kauyen Gadan dake karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano, wadanda yanzu haka suna jinya a asibitin Murtala Muhammad.
Dakta Aliyu Ibrahim ya jajanta wa wadanda abin ya shafa da kuma iyalansu.
Ziyarar ta Sarkin ta kasance a matsayin nuna tausayawa ga wadanda lamarin ya shafa.
Mai Martaba Sarkin ya jaddada muhimmancin hadin kai da goyon baya a tsakanin al’umma, inda ya bukaci a ci gaba da kokarin bayar da taimako ga mabukata.
Sarkin ya kara da cewa, tunaninmu da addu’o’inmu sun kasance tare da wadanda abin ya shafa da iyalansu yayin da suke samun kulawa da samun lafiya.
- Gwamnatin Jahar Kwara Ta Sanya Ranar Da Za Ta Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi.
- Gwamnatin Jahar Kwara Ta Sanya Ranar Da Za Ta Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi.
Dokta Aliyu Ibrahim ya tabbatar wa wadanda abin ya shafa cewa Masarautar za ta dauki nauyin duk wani magani da ake bukata domin samun sauki cikin gaggawa, sannan ta bayar da tallafin Naira miliyan uku ga wadanda abin ya shafa.
A nasa bangaren Hakimin Gezawa Mai Unguwar Mundubawa, Alhaji Mahmoud Aminu ya yabawa Sarkin bisa yadda ya nuna tausayi da goyon baya ga wadanda wannan lamari ya shafa.
Shima da yake jawabi shugaban riko na karamar hukumar Gezawa Hon Muhammad Bashir Tanko ya ce daga cikin mutane 25 da suka samu kuna, mutane goma sha uku ne suka mutu a halin yanzu, kuma mutane goma sha biyu suna kwance a asibitin Murtala Muhammad na musamman suna karbar kulawar lafiyarsu.
Hon Bashir Tanko, ya yi kira ga al’ummar yankin da su kasance masu lura da tsaro a kodayaushe, ya kuma kara da cewa majalisarsa za ta taimaka wa wadanda abin ya shafa da duk wani taimako da suka dace kuma nan ba da jimawa ba za su fara gyara Masallacin.