Ya zama wajibi Ministan Sadarwa,ya tabbatar ana amfani da fasahar zamani don yakar matsalar tsaro: Sarkin Kano

Spread the love

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya ce jazaman ne Ministan Sadarwa, Bosun Tijani, ya tabbatar ana amfani da fasahar zamani da kuma kwarewarsa wajen yakar kalubalen tsaro a Najeriya.

Sarki Aminu Ado Bayero wanda ya karbi bakuncin ministan a fadarsa a safiyar Alhamis, ya bayyana cewa minisan na da babban rawan da zai taka a yaki da matsalar tsaro, musamman a wannan yanayi da ’yan bindiga sun hana al’umma sakat.

“Da wayoyi ’yan bindiga da suke amfnai su yi magana da iyalan wadanda mutanen da suka sace, saboda haka akwai gagarumar gudummawar da ya kamata ma’aikatarka ta bayar wajen amfani da fasaha domin kamo su a hukunta su.

“Akwai bukatar ku yi amfani da fasahar zamani yadda ya kamata wajen yakar matsalar tsaro da ke kara tsanani a kasar nan, kuma mun san shugaban kasa yana da kwarin gwiwa a kanka shi ya sa ya ba ka wannan matsayi.

Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro

“Mu kuma a bangarenmu za mu ci gaba da yi maka addu’a domin samun nasara a wannan aiki,” in ji sarkin ga minstan wanda ke Kano domin halartar Babban Taron Majalisar Sadarwa, Kirkira da Tattalin Azikin Zamani ta Kasa (NCCIDE) karo na 11.

Da yake mayar da jawabi, ministan ya ba wa Sarkin Kano da al’ummar Najeriya tabbacin cewa zai yi iya kokarinsa wajen sauke duk nauyin da ya rataya a wuyansa.

“Da yardar Allah ba za mu yi kasa a gwiwa ba, wajen sauke wannan nauyi na al’umma da aka dora mana,” in ji ministan wanda ya samu rakiyarn manyan jami’an hukumomin da ke karkashin ma’aikatarsa.
Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *