Sarkin Kudan Muhammad Bello Haladu Ya Taya Mai Martaba Sarkin Zazzau Amb. Ahmad Nuhu-Bamalli Murnar Bikin Sallah Karama.

Spread the love

Sarkin Kudan Muhammad Bello Haladu Ya Taya Mai Martaba Sarkin Zazzau Amb. Ahmad Nuhu-Bamalli Murnar Bikin Sallah Karamar Sallah na shekara ta 2025.

Wannan Sanarwa data fito daga Wakilin Yada labarai na masarautar Kudan Malam Yusuf Ibrahim kudan tace Sarkin Kudan Muhammad Bello Haladu Ya jinjinawa Mai Martaba Sarkin na Zazzau bisa Kokarin sa Na ciyar da Masarautar Zazzau gaba.

Har ilayau wannan Sanarwa ta Kuma yiwa Mai Martaba sarki bangajiya bisa Ziyara Ta musamman dayakai garin na kudan Domin halartar Taron tallafawa Marayu Wanda ya bada nashi tallafi Mai tarin yawa, inda yace wannan ya shiga kundin Tarihin wannan gari.

Ya Kuma Kara jadda kudirin Masarautar ta kudan Karkashin masarautar ta Zazzau cigaba da goyon baya Domin Kara daukakan Masarautar ta Zazzau.

Sarkin na kudan ya Kuma yabawa Hakimai da dagatai na masarautar Zazzau bisa bisa goyon baya da suke Baiwa Mai Martaba sarki Musamman Hawa da aka Gudanar Mai Cike da Nasara.

Daga Karshe Sarki Muhammad Bello Haladu Ya Kuma jinjinawa Hakimai biyu Dake Karamar Kumar Kudan Chiritawan Zazzau Hakimin Hunkuyi Alhaji Aminu Muhammad Ashiru da Hakimin Kudan Tukuran Zazzau Bisa kokarin Da suke Wajen ciyar da yankin gaba.

Wakilin Yada labarai na masarautar Kudan
Malam Yusuf Ibrahim kudan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *