Sarkin Kudan Ya Taya Mai Martaba Sarkin Zazzau Murnar Cika Shekaru 5 Akan Karagar Mulki. 

Spread the love

 

Mai Girma Sarkin Kudan Alhaji Muhammad Bello Haladu ya jinjina tare da Taya Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Amb. Ahmad Nuhu Bamalli murnar cika Shekaru 5 akan karagar Mulki.

Wannan sakon Taya murnar da Sarkin ya aikewa Manema labarai ta fito ne ta hannun Wakilin Yada labaran Masarautar kudan Malam Yusuf Ibrahim kudan.

Sarkin na kudan Alhaji Bello Haladu yace Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli a cikin wadannan Shekaru 5 ya samu nasarori Masu tarin yawa.

Malam Bello Haladu yace Samun Nasara Mai martaba ya Samo asaline bisa jacircewa , da iya jagoranci da Kuma hidima ga Alummah Dake Masarautar Zazzau dama jihar Kaduna Baki Daya.

Sarkin Kudan yace a cikin wadannan Shekaru Mai martaba Sarkin Zazzau ya samu nasarar kyautata alaka da Hadin Kai a wannan Masarauta ta Zazzau, kana kokarinsa na inganta Rayuwar Alummah, a bangaren Ilimi, siyasa da tattalin Arziki sun bada Gudunmuwa wajen Samun wannan Nasara.

A bangaren Kyautata aluadu da zamantakewa Sarkin Kudan yace Mai martaba Sarkin Zazzau Yayi kokari wajen inganta da kyautata Al’adun mu na Masarautar Zazzau, ta hanyar bada goyon baya ga yan majalisar Sarki, Hakimai da dagatai Domin tabbatar da inganta Al’adun mu.

A kokarin sa na nunawa Alummar Masarauta ana tare Mai martaba Sarkin Zazzau yakan Dauki Lokaci don ziyatar Masaurautun Dake Kasar Zazzau Domin ganewa idanusa halin da suke ciki dama yadda suke tafiyar da harkar Sarauta.

Hakan yasa Alummar Garin kudan Bazasu taba mantawa da Ziyarar da Mai martaba Sarkin Zazzau yakai kudan ba inda Sarkin Kudan yace wannan ya shiga Kundin Tarihi na Wannan gari.

A wannan gaba Sarki Bello Haladu yace a madadin Alummar Masarauta kudan gaba Daya Yana Taya Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Amb Ahmad Nuhu Bamalli murna da cika Shekaru 5 akan karagar Mulkin Masarautar Zazzau tare da Fatan Alkhairi da Kuma Addu’ar Allah Ya karawa Sarki lafiya.

Wakilin Yada labaran Masarautar kudan.

Malam Yusuf Ibrahim kudan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *