Da alama za a tabbatar wa ƙasar Saudiyya damar karɓar baƙuncin gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa ta Duniya ta 2034, bayan FIFA ta amince da ƙoƙarinta wajen kare hakkin ɗan’adam a wani sabon rahoton tantance matsayinta kan kare haƙƙin bil-adama.
Hukumar ƙwallon ƙafa da Duniya FIFA ta bai wa ƙasar maki 4.198 cikin maki biyar – maki mafi yawa da aka bai wa ƙasashen da suka karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya a baya.
Duk da fargabar da ake da ita kan tarihin taƙe haƙƙin ɗan’adam a ƙasar, rahoton ya ce babu wata fargaba game da ‘yancin ɗan’adam a ƙasar.
Rahoton ya kuma ce gasar ka iya zama wani mataki na kawo sauye-sauye a fannin taƙe haƙƙin binl-adama a ƙasar.
Saudiyya ta kasance ƙasa ɗaya tilo da ke neman damar karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta 2034 bayan janyewar Australia a shekarar da ta gabata.
A wata mai zuwa ne ake sa ran FIFA za ta amince wa ƙasar karɓar baƙuncin gasar.