Sauya ministoci: Tinubu ya rushe wasu ma’aikatu, ya haɗe wasu.

Spread the love

A ranar Laraba ne shugaba Tinubu ya sanar da yin garambawul ga ministoci da ma’aikatun gwamnatinsa makonni kimanin uku da sanarwar yin sauye-sauye a gwamnatin tasa.

A wata takarda daga fadar shugaban ƙasa, shugaba Tinubu ya sallami ministoci guda biyar inda ya naɗa sabbi guda bakwai sannan ya sakewa wasu ma’aikatu su 10.

Dangane kuma da batun rusa da ƙirƙirar ma’aikatu, wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce an haɗe wasu ma’aikatun ne sannan an rushe wasu.

Bisa ga wannan sanarwa, gwamnati ta rushe ma’aikatu guda biyu sannan an ƙirƙiri hukumomi guda biyar inda kuma aka haɗe ma’aikatu guda uku.

Ministocin da aka sallama
Barista Uju-Ken Ohanenye – Ministar ma’aikatar mata
Lola Ade-John – Ministar yawon buɗe idanu
Farfesa Tahir Mamman – Ministan Ilimi
Abdullahi Muhamamd Gwarzo – Ƙaramin ministan gidaje da raya birane
Dr Ibrahim Bio Ibrahim – Ministan Matasa.

Sabbin ministocin da aka naɗa

Dr Nentawe Yilwatda – Ministan ma’aikatar jinƙai da yaye talauci.

Muhamamd Maigari Dingyaɗi – Minsitan ƙwadago.

Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu – Ƙaramar ministar harkokin waje.

Dr Jumoke Oduwale – Ministar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari.

Idi Mukhtar Maiha – Ma’aikatar kula da dabbobi.

Hon Yusuf Abdullahi Ata – Ƙaramin ministan gidaje da raya birane.

Suwaiba Said Ahmad phD – Ministar Ilimi
Ministocin da aka sauya wa ma’aikata.

Dr Yusuf Tanko Sununu – Sabon ministan ma’aikatar jinƙai.

Dr Morufo Olatunji Alausa – Sabon ministan Ilimi.

Barrister Barr. Bello Muhammad Goronyo – Sabon ƙaramin ministan ayyuka.

Hon Abubakar Eshiokpekha Momoh – Sabon ministan Hukumar raya shiyyoyin Najeriya.

Uba Maigari Ahmadu – Sabon ƙaramin ministan raya shiyyoin Najeriya.

Dr Doris Uzoka-Anite – Sabon ƙaramin ministan kuɗi.

Sen. John Owah Enoh – Sabon ƙaramin ministan masana’antu da zuba jari.

Imaan Sulaiman-Ibrahim – Sabuwar ministar harkokin mata.

Ayodele Olawande – Sabon ministan harkokin matasa.

Dr Salako Iziaq Adekunle Adeboye – Sabon ƙaramin ministan lafiya.

Yadda aka yi wa ma’aikatu garambawul
Ma’aikatun da aka rushe: Sanarwar ta Bayo Onanuga ta ce majalisar zartarwa ta rushe hukumar raya yankin Neja Delta wato Niger Delta Development Commission da ma’aikatar harkokin wasanni.

Sabbin ma’aikatu: Sanarwar ta ce majalisar zartarwar ta Najeriya ta amince da kafa sabuwar hukumar raya shiyyoyin ƙasar da za ta sa ido kan hukumomi biyar da suka haɗa da na raya shiyyar arewa maso yammaci da kudu maso yammaci da arewa maso gabashi da kudu maso gabashi da kuma Naija Delta.

Ma’aikatun da aka haɗe: Bayo Onanuga a sanarwar ya ce majalisar zartarwa ta amince a haɗe ma’aikatar harkokin yawon buɗe ido tare da ma’aikatar al’adu. Dangane kuma da ma’aikatar wasanni ta ƙasa, sanarwar ta ce yanzu hukumar kula da wasanni ta ƙasa ce za ta karɓe ayyukan ma’aikatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *