Kungiyar rajin kare dimokaradiyya da muradan al’umma wato SEDSAC ta yabawa gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa sanya Yan kungiyoyin farar hula cikin kunshin majalisar zartarwarsa.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Gwamnan jihar kano ya nada Amb. Ibrahim Abdullahi Waiya da
” Wannan matakin da gwamnan Kano ya dauka ya nuna cewa yana son tafiya da yan gwagwarmaya wanda suka dade suna taimakawa al’umma, Kuma hakan zai karawa gwamnatin kima a idanun duniya”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan kungiyar SEDSAC Kwamared Hamisu Umar Kofar Na’isa ya sanyawa hannu tare da aikewa manema labarai.
Sanarwar ta ce nada Amb. Ibrahim Waiya da Iro-ma’aji a matsayin kwamishinoni ba kawai abun yabo ba ne ga gwamnan, ya nuna yadda yake kishin dimokaradiyya da son cigaban Kano saboda ya zabo masu gaskiya da kwarewa ya sanyasu cikin gwamnatinsa.
Kungiyar ta SEDSAC ta taya yan gwagwarmayar murnar samun wannan mukami tare da bukatar su da su kara zage damtse don nuna kwarewa akan aikinsu don gudun kada su baiwa gwamna da sauran kungiyoyin farar hula Kunya.
- Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 10 A Wajen Rabon Tallafin Abinci A Abuja
- NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899