Serap ta buƙaci CBN ya yi bayanin ɓatan N100bn na kuɗin da suka lalace

Spread the love

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci gwamnan babban bankin ƙasar, Mista Olayemi Cardoso ya yi bayani kan ”yadda fiye da naira biliyan 100 na takardun kuɗin da suka lalace – da sauran kuɗi masu yawa da ke jiran tantancewa a rassan CBN ɗin – suka yi ɓatan dabo.

Cikin wata wasiƙa da ƙungiyar ta wallafa a shafnta na intanet, ta ce ta samu zarge-zargen ne cikin rahoton shekara-shekara da babban mai binciken kuɗi na ƙasa ya fitar a 2022.

“Rahoton babban mai binciken kuɗin na 2022 ya nuna cewa, tun a 2017 CBN ke ci gaba da taskance fiye da naira biliyan 100 na takardun kuɗin da suka lalace ko suka yi dauɗa, da wasu kuɗi masu yawa da ke jiran tantancewa a rassan CBN”.

Rahoton babban mai binciken kuɗin na fargabar cewa an karkatar, ko an sake maido da ”lalatattun takardun kuɗin da kuɗaɗen masu datti” da aka tsara cewa za a ƙone su.

Ƙungiyar ta ce zarge-zargen da ke cikin rahoton babban mai binciken kuɗin ya nuna yadda CBn din ya saɓa wa kundin tsarin mulki da dokar CBN da dokokin cin hanci na ƙasa da ma na duniya.

Haka kuma ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan na CBN ya yi ƙarin haske ”kan inda naira biliyan 7.2 da aka ware domin gina resehn bankin a Dutse a shekarar 2010, da kuma naira biliyan 4.8 da aka ware don sabunta resehn CBN na birnin Abeokuta a shekarar 2009.

Serap ɗin ta kuma buƙaci CBN ya wallafa sunayen ‘yan kwangilar da aka bai wa ayyukan, kuma suka gaza aiwatar da su.

Ƙungiyar ta kuma ce CBN din ya yi wa jama’a bayani kan wasu basukan da bankin ya bai wa wasu jihohin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *