Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta SERAP ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya soke sabon ƙarin kuɗin yin fasfo da hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanar, tana mai cewa hakan ya saɓawa doka kuma cin zarafin haƙƙin ɗan ƙasa ne.
Wannan na ƙunshe ne a wata cikin wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 30 ga Agusta, 2025, wacce mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu.
NIS ta bayyana cewa daga 1 ga Satumbar 2025, kuɗin yin fasfo mai shafi 32 na shekara biyar zai zama naira 100,000 yayin da na shafi 64 na shekaru goma kuma zai kai naira 200,000
SERAP ta ce wannan ƙarin zai hana talakawa da mutane marasa galihu damar yin fasfo zai kuma ƙara wahalar tattalin arziki da ake ciki.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa za ta kai ƙara kotu idan gwamnati ta ƙi soke wannan mataki cikin kwanaki bakwai.