Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa har yanzu Babban Kwamnadanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na nan kan kujerarsa bai yi murabus ba.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar, Sheikh Mujahid Aminuddeen Abubakar ne ya sanar da hakan.
Sheikh Mujahid ya bayyana haka ne bayan rade-radin da ke yawo cewa Sheikh Daurawa ya yi murabus, kan takaddamar sakin jarumar tiktok, Murja Ibrahim Kunya, daga gidan yari, bayan kotun Musulunci a ba da umarnin tsare ta.
A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa an fitar da Murja daga gidan yari, sabanin umarnin kotu, lamarin da ya haifar da damua a cikin al’umma.
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gama PRP a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare matashiyar a gidan yari ne ba bayan hukumar hisbah ta gurfanar da ita kan zargin karuwanci ga kananan yara, da kuma badala, zargin da ta musantarbiyya.
Alkalin kotun, Mai sharia Nura Yusuf Ahmad, ya bayar da umarnin tasa keyarta zuwa gidan yari tare da dage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu, 2024.
Da umarnin kotu muka sake ta —Gidan yari
Amma a bangarensa, kakakin gidan gyaran na Kurmawa, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya ce sun saki Murja ne tun a ranar Alhamis bayan da suka samu takardar umanin kotu a game da hakan.
A cewarsa, “Gidan yari na tafiya ne bisa dokoki, kuma dukn wanda aka tsare a gidan yari takarda ce take kai shi da sa hannun alkali, kuma takarda ke fitar da shi da sa hannun alkali.
“Muna da sa hannun dukkanin alkalan da ke Jihar Kano, dole sai alkali ya sa maka hannu sannan za a kawo ka, haka ma dole sai ya sa hannu kafin a fitar da kai.
“A takaice kotu ce ta kawo Murja, ita ce kuma ta fitar da ita,”
Yau Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ramlat ’Yar TikTok
MAI MAGANA DA YAWUN KOTUNAN MUSULINCI A Kano Kakakin Manyan kotunan shari’ar addinin musulinci na jahar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa rade-radin da ake ta yi cewar Murja Kunya, an sake ta ko an bada ita beli , magana ta gaskiya Murja, ta na waje tun ranar Alhamis.
Mizammil Ado Fagge ya ce sun tuntuni kotun da ake yin shari’ar , inda ta shaida mu su cewar, Lauyoyin ma su gabatar da kara ne , suka zo suka ari Murja , domin ci gaba da tuntubarta kan wani zargi dake kara bibiyarta.
” Amma ba abun mamaki ba ne dan an bayar da belin Murja Kunya, saboda na farko wannan laifi da ta yi ba laifi ba ne wanda za a ki bayar da ita beli” Muzammil Fagge”.
Ya kara da cewa, Hurimin kotu ne na ta bada beli ko ta hana , amma dai magana ta gaskiya Murja ba ta gidan gyaran hali tun ranar Alhamis.
” wannan ba sabon abu ne, sai dai kawai ita saboda labarin ya ya mutsa hazo kuma ga abubuwan da ta ke yi , wanda ya saba da al’ada da kuma addinin mu na Musulinci shi yasa mutane kowa hankalina ya tafi akai”.
Hurumin hukumar Hisbah
Hukumar Hisbah, wadda ta kama Murja, ta ce ita aikinta shi ne ta kama mutum, amma ba ta da hurumi kan yanke masa hukunci ko fada wa alkali irin hukuncin da zai yi masa.
Haka kuma Hisba ta ce wannan abu da ya faru ba zai sa ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Al’umma dai na ci gaba da lugudan labba musamman a shafukan sada zumunta kan wannan lamari.