Sheik Abduljabbar Nasir Kabara ya baranta kansa da daukaka karar da wasu Dalibansa suka yi.

Spread the love

Sheik Abduljabbar Nasir Kabara, ya mayar da martani kan wasu mutane da suka daukaka kara a babbar kotun jahar Kano, da cewar ba Daliban sa ba ne masu zalintar sa ne.

Abduljabbar Kabara ya bayyana hakan ne ta cikin wasika da ya rubuta ya kuma sanya hannu kan takardar, mai kwanan watan 7 ga watan Fabarairun 2024.

‘’ Game da sabon Appeal wanda na samu labarin, wasu mutane sun shigar da shi da sunan wai Dalaibai na su, ina sanar da duniya cewa wadannan mutane basa tare dani a wannan rintsin’’ Sheik Abduljabbar  Kabara’’.

Idongari.ng facebook link https://www.facebook.com/profile.php?id=100089819831293

An ceto mutum 20 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina

Majalisar wakilan Najeriya za ta ƙarfafa dokar ɓata-suna

Abduljabbar Ya kara da cewa, wadannan mutane sun daukaka kara ne domin su lalata masa appeal din, da ya shigar tun a ranar 23 ga watan Disamba 2023, don su zalince shi.

An gurfanar da Abduljabbar Nasir Kabara, a gaban babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake Kofar Kudu gidan sarki a jahar Kano, bisa tuhumar sad a aikata yin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wassalam, inda kotun ta same shi da aikata laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar raya.

Tun daga ranar 15 ga watan Disamba 2022, da yanke hukuncin ne ya daukaka kara a ranar 23 ga watan Disamba 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *