Kotun Daukaka Kara: Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara Ya Nemi Gwamnatin Kano Ta Biya Shi 20m.

Spread the love

Kotun daukaka Kara dake zaman ta a sakatariyar Audu Bako Kano, ta dage ci gaba da sauraren shari’ar da Abduljabbar Nasir Kabara, da ya daukaka kan hukuncin kisa ta hanyar rataya, da babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Kofar Kudu Kano, ta yanke masa bisa samun da laifin yin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammed Sallallahu Alaihi Wassalam.

Kotun daukaka karar karkashin jagorancin, justice Nasiru Yusuf da kuma A’isha Mahmud , sun saurari karar a Ranar Litinin.

Jaridar idongari.ng ta ruwaito cewa, lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, Barista Yusuf Sadik, ya shaida wa kotun cewar a shirye suke don ci gaba da sauraren shari’ar.

Sai dai lauyan gwamnatin Kano Barista Bashir Saleh, ya roki kotun da ta Kara mu su lokaci Kafin a ci gaba da sauraren shari’ar.

Lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya nuna rashin jin dadinsa , sakamakon ya tun tuni ya sada lauyan gwamnatin da takaddun martaninsu tun a watan Fabarairun 2024, inda ya nemi gwamnatin Kano ta biyashi naira miliyan 20 , sakamakon bata masa lokaci da aka yi.

Alkalan kotun , Justice Nasiru Saminu da Justice A’isha Mahmud, sun bincika takaddun da lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya yi ikirarin ya sadar da lauyan gwamnatin Kano, inda aka gano cewar a watan Maris ya ba wa lauyan gwamnatin takaddun martanin .

Daga bisani lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya janye bukatar Neman Gwamnatin ta biya shi naira miliyan 20, kamar yadda jaridar idongari.ng, ta ruwaito.

Alkalan kotun daukaka karar sun dage ci gaba da sauraren shari’ar, zuwa Ranar 9 ga watan Mayun 2024, don ci gaba da sauraren shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *