‘’Da ƙyar nake ɗaukar ɗawainiyar iyalina,” in ji wani soja mai muƙamin kofur a Najeriya a lokacin da yake zantawa da BBC Hausa, inda yake bayyana yadda tsananin tsadar rayuwa take shafar sojojin ƙasar.
Aikin soja wani aiki ne da ake ganin ya fi kowane aikin ɗamara ƙima, amma duk da ƙimarsa, Hausawa sukan yi masa kirarin ‘marmari daga nesa.”
Shi dai wannan sojan mai suna Ibrahim (ba asalin sunansa ba) ya bayyana cewa yadda abubuwa suka lalace, musamman yadda abubuwa suka yi tsada saboda taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa da tsadar rayuwa, suma sojojin suna buƙatar a kula da rayuwarsu kamar yadda suke tsare ƙasar.
“Maganar gaskiya a yanayin tsadar rayuwa da ake ciki, albashin nan ba zai isa mutum ba. Ko kaɗan wannan albashin ba zai isa mutum ciyar da iyalinsa ba, ballantana ya ce zai yi sauran ɗawainiya da suka shafi buƙatun rayuwa,” in ji sojan mai muƙamin kofur wanda yake aiki a wata jiha a Arewa maso Yamma.
A game da albashin da yake karɓa, sojan ƙasan ya ce, “yanzu da nake da muƙamin kofur wato mai igiya biyu, ina karɓar albashin naira 59,500 ne. Dama albashin kofur yana tsakanin naira 59.300 ne haka zuwa naira 60,000,” in ji sojan wanda ya yi sama da shekara 10 yanzu yana aiki.
Ya ƙara da cewa soja na samun ƙarin albashi ne ta hanyar samun ƙarin girma wato ƙarin igiya, inda ya ce sabon soja yana samun igiya ɗaya ne bayan shekara biyar, sannan ya samu igiya na biyu bayan ya yi wani aikin na shekara biyar, “mutum zai kai muƙamin kofur ne bayan ya yi aikin shekara goma,” in ji shi.
Sai ai ya ce akwai alawus da ake ba sojojin da suke fagen da ake kira Ration Cash Allowance wato RCA a taƙaice, “shi ma ya danganta da yanayin wata. Idan wata mai kwana 30 ne, ana biyan naira 35,500, idan kuma wata ne mai kwana 31, ana biyan naira 36,500.”
Sai dai sojan ya ce duk da cewa da alawus ɗin ne suke ‘rage zafi’, wani lokacin sai a haɗa biyu zuwa uku ba a biya ba, “sai daga baya a ɗan biya bashin wasu watannin,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa rayuwa ga wanda yake aikin soja, musamman wanda yake da ɗawainiyar iyali, sai dai kawai ya yi da haƙuri.
Shi ma wani sojan wanda ba shi da igiya, ya bayyana cewa rayuwar aikin soja sai a hankali.
“Kasancewar ni ba ni da mata, sai dai iyaye kawai da ƴanuwa. Wannan ya sa nake lallaɓawa da abincin da ake kawo mana, kasancewar gaskiya mu dai ana kawo mana abinci. Wannan ya sa nake iya ajiye wasu ƴan kuɗaden kasancewar ina bi a hankali matuƙa wajen gudanar da rayuwar.
“Ina wajen aikin soji na musamman ne wato operation, to ina samun alawus. Ka ga ba za a haɗa kuɗin da nake samu da wanda yake aiki a ofis a gida ba,” in ji shi.
Game da yadde rayuwa take, ya ce”Ka san kowa akai yadda ya tsara rayuwarsa, kuma ba kowa ba ne yake samun abin da yake so a rayuwa. Kawai muna amfani da abin da muke samu ne. Sannan kuma ya danganta da yanayin kashe kuɗin mutum, musamman waɗanda ba su da hidimar da ta zama dole.
“Amma uwa-uba shi ne maganar gaskiya duk wanda yake so ya cimma wani abu a rayuwa, dole sai ya haƙura da wasu abubuwan.”
Za a yi ƙarin albashi – Hedkwatar tsaro
A game da yanayin albashin sojojin, musamman yadda wasu suke ganin ya yi kaɗan, BBC ta tuntuɓi kakakin hedkwatar tsaro na Najeriya, Janar Tukur Gusau, inda ya ce kusan kowa a Najeriya ya san halin da masu karɓar albashi suke ciki.
A cewarsa, “Gaskiya haka ne, ba wai sojoji ba kawai, kusan duk wani mai amsar albashi zai iya cewa yanayi na tsadar rayuwa ya sa albashinsa ba zai biya masa buƙatunsa ba. Abun da zan iya faɗa shi ne, na san cewa gwamnati na ƙoƙari ta ga an ƙara albashi na sojoji da sauran jami’an tsaro,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa yana ƙoƙari domin tabbatar da ƙarin albashi.
Sai dai ya ce, “Kamar yadda kuka sani ba hukumar soja ba ce ke biyan albashi, inda ake biyan kowane ma’aikacin gwamnatin tarayya albashi, haka muma ake biyanmu albashi daga ofishin akanta janar. Don haka muna fata za a mana ƙarin albashin,” in shi.
A game da alawus na RCA kuwa, cewa ya yi, “gaskiya wannan maganar sabuwa ce a gare ni, ban sani ba. Na san shugabanmu, Janar Christopher Gwabin Musa a kullum ƙoƙari yake yi wajen tabbatar da cewa kowane soja da yake fagen daga yana samun haƙƙoƙinsa kamar yadda ya dace. Amma za mu bincika, kuma idan muka tabbatar da matsalar, ina tabbatar maka za mu ɗauki tamakin da hakan zai sake faruwa ba.”
BBCH