Shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika da wani ɗan uwansa, Ahmad Sirika, a yau talata a wata sabuwar shari’ar kan badakalar kwangilar da ta kai naira biliyan 19.4 ya samu tsaiko sakamakon rashin kasancewarsu a gaban alƙali.
Gidan talbijin na Channels TV ya ce lauyan Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya shaida wa alkalin kotun, Mai shari’a Suleiman Belgore, cewa ba a sanar da tsohon ministan da dan uwansa abin da ake tuhumar su ba, a shari’ar.
Don haka lauyan ya buƙaci a ɗage shari’ar, buƙatar da alkalin ya amince da ita.
Daga baya alƙalin ya sanya ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gurfanar da su gaban kotu.
- Mutanen da baƙuwar cuta ta yi ajalinsu a Zamfara sun kai 13
- Kano: Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Mutane 17 Hukunci Bisa Samun Su Da Laifin Siyar Da Kudaden Wajen Ba Tare Da Lasisi Ba.
Hukumar EFCC na tuhumar tsohon Ministan ne da ɗan uwansa a wannan karon, da abubuwa takwas da suka jiɓanci tsabar kuɗi har naira biliyan 19.4.
Adadin dai an ce na wasu kwangilolin ma’aikatar sufurin jiragen sama ne daga tsohon ministan zuwa kamfanin Enginos Nigeria Limited wanda ake zargi mallakar ƙanin nasa ne.
A makon da ya gabata ne aka gurfanar da Sirika da diyarsa Fatima da kuma sirikinsa a gaban kotu kan zargin badaƙalar naira biliyan 2.7, inda daga bisani kotu ta bayar da belinsu.