Shugaba Tinubu Ya bayar Da Umarnin Horas Da Matasa Miliyan 5 Sana’o’in Dogaro Da Kai Kowacce Shekara. ( ITF)

Spread the love

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin horas da matasa miliyan biyar, sana’o’in dogaro da kai kowacce shekara.
Babban Direktan hukumar bayar da horon sana’o’in dogaro da kai, Industrial Training Fund (ITF), na kasa, Dr. Afiz Ogun Oluwatoyin, ne ya bayyana hakan, ya yin gabatar da shirin , Skill Up Artisants wato ( SUPA) a birinin tarayya Abuja.
Jaridar Idonagri.ng, ta ruwaito cewa, shirin na ITF an tsara shi, don horas da matasa dubu dari 100,000 wanda za a fara horaswar a karshen watan Yunin 2024.

Dr. Afiz Oluwatoyin, ya kara da cewa matasan Nigeria an barsu a baya kan sana’o’in dogaro da kai, duk da cewar matasan suna da fasahar gudanar da sana’o’in.

Sai dai ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu yan kasashen ketare, suke amfana da kayan da suke samarwa, sakamakon rashin karfafawa matasan gwiwa don dogaro da kananan sana’o’in dogaro da kai, da zai habbaka tattalin arzikin yankunansu da rage fatara da zaman banza.

Ya ce dukkan maatsan da za a horas za su tabbatar sun samu aikin yi don dogaro da kai, wanda matasa maza da mata za su amfana da shirin, ta hanyar ba su shaidar da za ta taimaka mu su har a kasashen waje.

Danna wannan link supa.itf.gov.ng domin cike shirin supa na ITF.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *