Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya sauke Sha’aban Ibrahim Sharada daga shugabancin hukumar kula da almajirai ta Najeriya.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Janar Ja’afar Isa jagora ne nagari ya kuma taba zama gwamnan jihar Kaduna da kakin soji daga 1993 zuwa 1996, yayin da Alhaji Tijani Hashim Abbas shi ne Sarkin Sudan Kano.
Hukumar Kwastan Ta Kama Muggan Kwayoyi Da Makamai A Tashan Jiragen Ruwa ta Legas
Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Alhaji Tijjani Hashim Abbas a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masarautu.
Shugaban ƙasar ya yi hasashen cewa sabbin wadanda aka nada din za su yi amfani da gogewar da suke da ita wajen gudanar da aiyukan da aka dora musu don cigaban al’ummar Nigeria.
Lawan Jafaru Isa da Alhaji Tijjani Hashin Abbas dukkaninsu sun fito ne daga jihar kano.