Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin dakatar da harajin 0.5 na tsaron intanet – ko kuma cybersecurity levy a Turance.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya faɗa wa manema labarai cewa an ɗauki matakin ne bayan muhawarar da majalisar zartarwa ta yi a yau Talata.
Sai dai ya ce shugaban ya ba da umarnin a sake duba tsarin da kuma yadda za a aiwatar da shi.
Tun a ranar 6 ga watan Mayu Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da harajin kuma ya umarci bankuna su fara karɓar kashi 0.5 cikin 100 na kuɗaɗen da ‘yan ƙasa suka tura tsakanin asusan ajiya cikin mako biyu.
- Jami’an DSS Sun Yi Kunnen Kashi Da Umarnin Alkali Kan Hana Su Yin Kame A Harabar Kotu
- An kama riƙaƙƙun ƴan fashi’ da ake zargi da yaudarar mutane a Nasarawa