Shugaban ƙasar Chadi ya fara yaƙin neman zabe

Spread the love

Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya fara yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a ranar Lahadi, gabanin zaɓukan da za a gudanar da nufin tafiyar da ƙasar bisa tsarin mulkin farar hula na dimokuraɗiyya.

Shugaban zai dai fuskanci wasu ƴan takara tara a zaɓen da aka shirya yi a ranar 6 ga watan Mayu, ciki har da firaminista Sucés Masra da aka naɗa.

Shugaban ya kuma miƙa saƙonsa na farko a taron yaƙin neman zaɓensa a babban birnin N’Djamena.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, yayin da yake jawabi ga taron, shugaban wanda tsohon soja ne, ya jaddada ƙudirinsa na cika alƙawuran da ya ɗauka.

Deby ya bayyana alƙawuran yaƙin neman zaɓensa, inda ya mayar da hankali wajen inganta matakan tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar Chadi.

Hasashe dai ya dabaibaye takarar Mista Déby, inda da dama ke sa ran zai samu nasara a zaɓen, ko da yake wasu ƴan adawa sun soki tsarin zaɓen da cewa “almara ce.”

An kashe babban abokin hamayyarsa, madugun ƴan adawa Yaya Dillo a wata musayar wuta da jami’an tsaro a ranar 28 ga watan Fabrairu inda gwamnatin ƙasar ta danganta mutuwar tasa da zargin hannunsa a wani mummunan hari da aka kai kan hukumar tsaron ƙasar, lamarin da ya musanta.

Haka kuma kotun tsarin mulkin ƙasar ta kuma haramta wa wasu ‘yan takara 10 takara a watan da ya gabata, ciki har da wasu masu sukar lamirin gwamnatin ƙasar.

Da farko dai shugaba Deby ya yi alƙawarin miƙa mulki bayan watanni 18 ga mulkin dimokraɗiyya bayan hawansa mulki a shekarar 2021, bayan rasuwar mahaifinsa.

Amma daga baya ya ɗage zaɓen har zuwa wannan shekarar, lamarin da ya janyo zanga-zangar da jami’an tsaro suka dakile da karfin tsiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *